✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Saudiyya: An kwantar da Sarki Salman a asibiti

Rahotanni na bayyana cewa an kwantar da sarki Salman Bn Abdul’aziz na Saudiyya saboda lalurar da ya samu a mafitsararsa. Sarki Salman ‘Dan Abdul’aziz na…

Rahotanni na bayyana cewa an kwantar da sarki Salman Bn Abdul’aziz na Saudiyya saboda lalurar da ya samu a mafitsararsa.

Sarki Salman ‘Dan Abdul’aziz na kasar Saudiyya ya na kwance a asibiti da ke birnin Riyadh ana yi masa gwaje-gwaje, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka sanar.

Jaridun kasar Saudiyya a ranar Litinin, sun tabbatar da cewa an kwantar da sarkin mai shekara 84 a asibiti.

Sarki Salman ya fara mulki a Saudiyya tun a shekarar 2015 kafin zamansa Sarki. Kuma ana ci gaba da yi masa gwaje-gwaje

Kamfanin dillacin labaran kasar Saudiya SPA ya bayyana cewa an kwantar da Sarki Salman asibitin birnin Riyadh, ba tare da wani cikakken bayani ba.