Mahukunta a kasar Saudiyya sun wajabta wa maniyyata aikin Hajji da Umrah yin allurar rigakafin COVID-19.
Ministan Aikin Hajji da Umrah na Saudiyya, Muhammad Saleh Benten ya bayyana hakan ne bayan an yi masa allurar rigakafin cutar.
- Masu Umrah sun rasu a hanyar zuwa Makkah
- An ceoto mutum 77 daga masu garkuwa a Katsina
- Boko Haram ta yi garkuwa da Hakimi a Yobe
- Sarakuna ke gayyato ’yan bingida —Gwamnan Neja
“Duk wanda ke son yin aikin Umrah ko Hajji dole ne ya yi allurar rigakafin,” inji Ministan.
Ya ce daukar matakin ya zama tilas domin kare yaduwar annobar a tsakanin mahajjata.
Ya kara da cewa za a ci gaba da daukar matakan kariyar cutar da suka hadar da wanke hannaye da sanya takunkumi da kuma ba da tazara.
Wannan mataki na kasar Saudiya na zuwa ne a lokacin da maniyyata da ke sa ran yin Umrah ke yin harama.