Gwamnatin Saudiyya ta kori jami’anta da dama kan saba wa ka’ida a kwangilar wani katafaren aikin gini da take gudanarwa na biliyoyin kudi.
Kamfanin dillancin labarai na kasar SPA, a ranar Juma’a ya ruwaito cewa, gwamnatin ta kuma kaddamar da bincike kan jami’an da ta kora wadanda da ta dora wa alhakin kula da aikin.
Ana zargin jami’an da saba wa ka’ida sakamakon ba da izinin dasa gine-gine a wuraren da ba su cancanta ba wanda hakan zai iya haifar da nakasu a ingancin ginin ta yadda ba zai yi karko ba.
Manyan jami’an da aka kora kamar yadda dokokin kasar suka tanada sun hadar da Darekta Janar mai kula da iyakokin kasar da Gwamnonin biranen Umluj da al-Wajh da shugabannin iyakokin biranen biyu.
Sauran jami’an da aka sallama sun hada da masu kula da kan iyaka a lardunan Madina, Tabuka da Assir.
Shekaru uku da suka gabata gwamnatin Saudiyya ta bayyana kudirin aiwatar da gina katafaren birni da zai dauki wuraren yawon bude ido da shakatawa na tarihi da kuma harkokin kasuwanci a yankin Bahar Maliya.
Yariman Saudiya, Mohammed bin Salman, shi ne ya kawo wannan tsari domin fadada hanyoyin samun kudi a kasar mai arzikin man fetur.