✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Press To Play

Sau nawa aka taba soke gudanar da Aikin Hajji a tarihi?

Daga nan aka dakatar da aikin Hajji na tsawon shekara 10 a Makka....

Annobar COVID-19 da ake fama da ita a halin yanzu a duniya ta janyo takaita adadin alhazan da za su gudanar da aikin Hajj a karo na biyu kenan a jere.

Takaitawar ta haifar da karuwar yada ‘labarun karya’ da ma ‘kagaggun shaci-fadi’ na rashin hankali, duk kuwa da cewa an dauki matakin ne bayan dogon nazari a tsawon watanni tare da la’akari da sababbin bayanan da aka tattara kan yaduwar cutar da zimmar kare lafiyar mahajjatan har ma da duniya baki daya.

A wannan mukalar, mun tattaro adadin lokutan da aka kayyade aikin Hajji bisa dalilai da dama, amma mafi yawansu sun kasance ne saboda barkewar wata cutar ko annoba.

Ko da yake an soke aikin Hajji sau da yawa a cikin karnoni, tun lokacin da aka kafa Masarautar Saudiyya a 1932, an hana Hajji sau biyu ne kacal wato a 2020 da 2021.

865: Kisan kiyashi a Dutsen Arafat

A lokacin rigimarsa da Khalifancin Abbasawa da ke Bagadaza, Ismail bin Yousef, wanda aka fi sani da Al-Safak, ya kai hari a kan dutsen Arafat mai tsarki da ke fuskantar birnin Makka a shekara ta 865, inda ya yi wa mahajjata kisan gilla a can. Rikicin ya tilasta dakatar da aikin Hajji.

930: Harin Qarmatian

A shekarar 930, Abu Taher al-Janabi, jagoran darikar Qarmatian da ke da mazauni a Bahrain, ya kaddamar da hari a kan birnin Makka.

Tarihi ya nuna cewa ’yan Qarmatian sun kashe mahajjata 30,000 a cikin birnin Makka mai alfarma sannan suka jefar da gawawwakin a cikin rijiyar Zamzam mai alfarma.

Sun kuma yi wasoso a Babban Masallacin Harami tare da satar Dutsen Hajarul Aswad daga cikin Kaaba, sannan suka kai shi tsibirin Bahrain.

Daga nan aka dakatar da aikin Hajji na tsawon shekara 10 har sai da aka dawo da Dutsen na Hajarul Aswad zuwa Makka.

’Yan Qarmatian din mabiya mazhabar Shi’a ne wadanda suka yi imani da tsarin al’umma ta daidaito kuma suka yi imanin cewa aikin hajji al’adar arna ne.

983: Halifancin Abbasid da Fatimid

Ita ma siyasa, ta sha dagula aikin Hajji.

A cikin rikice-rikicen siyasa na 983 tsakanin sarakunan halifofi biyu – Abbasiyawa na Iraki da Siriya da Fatimiyawa na Misira – sun haifar da cikas ga Musulmin da ke tafiya Makka domin aikin Hajji. Sai da aka shafe shekara takwas kafin a sake gudanar da aikin Hajji wato sai a cikin 991.

1831: Annoba

Ba wai kawai rikice-rikice da kashe-kashe ne suka sanya soke aikin Hajjin ba.

Wata annoba daga Indiya ta afka wa birnin Makka a 1831, inda ta kashe kashi uku cikin hudu na mahajjata a wurin, wadanda suka jure wa wahalhalun tafiya cikin kasashe da hanyoyi masu matukar hadari na tsawon makonni domin kawai su kai ga gudanar da aikin Hajji.

1837-1858: Faruwar annoba a jere

A cikin kusan shekara 20, an dakatar da aikin Hajji sau uku, wanda ya haifar da mahajjata ba sa iya zuwa Makka na tsawon shekara bakwai.

A cikin shekarar 1837, wata annoba ta sake bulla a birnin Makka mai tsarki, inda ta tsayar da komai a ciki har zuwa shekarar 1840.

Sannan a cikin shekarar 1846 wata mummunar cutar Kwalara ta afka wa birnin Makka, inda ta kashe sama da mutum 15,000, kuma ta ci gaba da addabar mazauna birnin har zuwa 1850.

Annobar ta sake barkewa a shekarar 1865 da kuma 1883.

A shekarar 1858, wata annobar kwalarar da ta gallabi duniya ta shiga birnin Makka, wanda hakan ya sa mahajjatan Masar suka gudu gaba daya zuwa gabar tekun Bahar-Maliya, inda aka killace su a wajen.