Wata babbar kotu a Kano ta bayar da umarnin kamo wasu mutum uku da ake zargi da kin bayyana a gabanta don amsa tuhuma akan satar yara.
Wadanda ake tuhumar sun hada da wata mata da ake zargi da hada baki da wasu mutum bakwai wajen aikata laifin.
- A Kano za a kai limaman Juma’a 15 kotu
- Kotu ta umarci Gwamnatin Kano ta mayar da ma’aikatan lafiya bakin aikinsu
Sa dai zaman kotun na Mai Shari’a Dije Aboki ya samu tsaiko saboda daya daga cikin mutum bakwai da ake zargi da hada baki ba ta jin Turanci ko yaren Pidgin, sai dai yaren Igbo kawai.
Lauya mai gabatar da kara, Barista Tijjani Ibrahim ya nemi kotun ta yanke hukunci a kan sauran wadanda ake zargin wadanda da ma ta ba da belinsu.
Mai Shari’a Aboki ya bukaci gwamnain jihar Kano da ta samar da mai tafinta a zaman kotun na gaba wanda ya dage zuwa 25 ga Nuwamba.
Aminiya ta ruwaito cewa ana zargin mutanen ne da hada baki da wasu suka sace wani yaro mai shekara 2 wanda ya mutu a hannunsu, kuma hakan laifi ne a sashi na 97 da 273 na kundin laifuka.
Wadanda ake zargin an kamo su ne a unguwar Kawon Lambu ‘B’ a Karamar Hukumar Nassarawa da ke Jihar Kano a 2017.