Wata Kotun Majistare da ke Ota a Jihar Ogun, ta yanke wa wani mutum mai suna Adungba Taiwo mai shekara 47 hukuncin daurin watanni takwas a gidan yari bisa samunsa da laifin satar kofofin karfe 34 da kudinsu ya kai N805,000.
Mai laifin, ya ki amsa laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban kotun.
- Yadda ake bude makarantun kudi a Kwara abin damuwa ne – Majalisa
- Dan mawaki Davido mai shekara 3 ya rasu
A hukuncin da ta yanke, Alkalin kotun, Mai Shari’a A.O. Adeyemi, ta yanke wa wanda ake tuhuma hukuncin tare da zabin biyan tarar N5,000.
Ta kuma bukaci mai laifin da ya mayar da N805,000 ga wanda ya shigar da karar.
Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara, Insifekta E.O. Adaraloye, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 22 ga watan Satumba da misalin karfe 5:00 na yamma a yankin Arima da ke garin Ota.
Adaraloye ya ce mai laifin ya karbi kofofin karfe 35 daga hannun wanda ya kai karar, da nufin zai biya daga baya.
“Amma maimakon cika yarjejeniyar da ke tsakaninsu, sai ya mayar da kudin zuwa amfanin kansa,” in ji shi.
Ya ce laifin ya ci karo da sashe na 390 na Kundin Laifuffuka na Jihar Ogun, na shekara ta 2006.