Wata kotun Majistare ta daure wani matashi mai shekara 22 a gidan yari na tsawon shekara daya bayan ta kama shi da laifin zamba da kuma satar wayar salula kirar iPhone.
Alkalin kotun, Mai Shari’a A.A. Ayeni, yayin da yake hukunci ya kama wanda ake zargin da aikata laifukan sata da zamba cikin aminci.
- Mahara sun yi awon gaba da Hakimi a Adamawa
- Zamfarawa sun yi artabu da ’yan bindiga har maboyarsu
- Matar aure ta kashe budurwar da mijinta zai aura
Mai Shari’a Ayeni, ya kuma ba shi damar zabar biyan kudi N10,000 kan kowane laifin da ake cajin sa da shi.
Tunda farko, dan sanda mai gabatar da kara, Sunday Osanyintuyi, ya fada wa kotu cewa matashin ya sace wayar salula guda daya, kirar iPhone 8plus, da ta kai kimar kudi N166,000 mallakar Adediwura Ogunleye.
“Har-ila yau, ana zarginsa da zambar kudi N50,000 na wani mutum daban mai suna Shittu Samuel, inda ya zambace shi da sunan zai biya masa kudin hayar gidan da yake zaune, amma ya kashe N50,000 din mutumin a sabgar gabansa,” inji shi.
Ya ce matashin ya aikata laifin ne a ranar 18, ga watan Nuwambar 2020 da misalin karfe 11 na safe a unguwar Mayfair dake Ile-Ife.
Osanyintuyi, ya kara da cewa aikata hakan ya saba da sashe na 383,390 (9) da 419 na kundin dokokin hukunta masu laifin na Jihar Osun, 2002.