Wata kotun Majistare da ke zamanta a garin Kwadon a Jihar Gombe ta aike da wani manomi mai shekara 28 a duniya zuwa gidan yari bisa laifin satar dan taure.
An dai gurfanar da manomin, mazaunin Garin Waziri na Karamar Hukumar Yamaltu Deba na jihar ne bisa zargin keta iyaka da kuma sata.
Rahotanni sun mutumin ya aikata lafin ne da tsakar daren 12 ga watan Agusta, inda ya fasa gidan wani mai suna Tela Yahaya sannan ya saci wani dan taure da darajarsa ta kai kusan N10,000.
Wanda ake zargin dai ya amsa laifin da aka tuhume shi da aikatawa.
Tun da farko dan sanda mai gabatar da kara, Kofur Abba Mathias ya shaida wa kotun cewa laifin ya saba da sashe na 286 na kundin dokar Penal Code.
Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Bala Ciroma ya aike da mutumin zuwa gidan yari na tsawon shekaru uku ko kuma biyan tarar Naira dubu dari biyu.
Kazalika, kotun ta kuma umarce shi da ya biya mamallakin dan tauren N15,000.