✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar daliban Kaduna: Iyaye da dalibai sun tare hanya

Sun yi barazanar ci gaba da rufe titi har sai gwamnatin jihar ta biya bukatarsu.

Iyayen da aka yi garkuwa da ’ya’yansu 39 a Kwalejin Gandun Daji ta Tarayya da ke Afaka, Jihar Kaduna sun tare hanyar zuwa filin Jirgin sama da Kaduna, a ranar Litinin.

Kimanin mako biyu ke nan da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da dalibai 39 a kwalejin, lamarin da ya sa iyaye da daliban da suka kubuta gudanar da zanga-zangar lumana.

Matakin da iyayen daliban suka dauka na tare hanyar filin jirgin a ranar Litinin ya haifar da cunkoson ababen hawa.

Iyayen daliban sun yi hakan ne don jawo hankalin gwamnatin jihar, wajen ceto ’ya’yansu daga hannun ’yan bindigar.

Masu zanga-zangar lumanar sun yi amfani da manya-manyan abubuwa wajen rufe hanyar, wanda haka yasa matafiya shiga tasku.

Daga baya sojoji da ’yan sanda sun yi nasarar lallashinsu aka bude hanyar da suka rufe.

Mista Friday Sani, wanda ya wakilci iyayen wajen tattauna da wakilinmu, ya bayyana cewa, “Mun gaji da shirun gwamnati kan satar daliban nan, saboda yawancin ’yan matan ba su da wani kayan kirki yayin da aka sace su”.

Sannan ya bukaci gwamnan jihar, Nasir El-Rufai da ya canja ra’ayinsa na kin yin sulhu da ’yan bindiga, wanda a cewarsa ceto rayuwar yaran ya kamata a sa a gaba fiye da komai.

Sun kuma yi barazanar ci gaba da zama a kan titi har sai bukatarsu ta biya.