Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ya ce yawan kai hare-hare da kuma garkuwa da mutane na barazana ga ilimin yara musamman mata a Arewacin Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a Abuja yayin wani bikin bajekolin zane-zane da hotuna irinsa na farko da dan Sanata mai wakiltar Adamawa ta Kudu, Sanata Binos Dauda Yaroe, wato Stephen ya shirya.
Makarantu da dama ne dai a Arewacin Najeriya suka fuskanci hare-haren ’yan bindiga yayin da aka sace daruruwan dalibai.
Sanata Ahmed Lawan ya ce, “Dama ilimi na fuskantar kalubale a Arewacin Najeriya, wanda a yanzu kuma matsalar tsaro ta kara tabarbara shi, inda ake satar daliban makarantun boko da na Islamiyya. Yanzu haka matsalar ma ta tasamma zama ruwan dare.
“Matsalar ta shafi har manyan makarantu. Ya zama wajibi mu tashi tsaye mu yaki wannan matsalar ko zaman lafiya ya dawo mu samu ci gaban kasa.”
Ya ce matsalar tsaron kalubale ne da ya zama wajibi gwamnatoci a kowanne mataki su hada karfi da karfe domin a lalubo bakin zaren.
A cewarsa, “Ina so in tabbatarwa kowa cewa wannan babban kalubale ne da yake bukatar hada hannu kafin a magance shi. Dole sai muna raye za mu iya cimma kowanne irin burin da muke da shi.
“Ba karamin abin takaici ba ne yadda harkar tsaronmu ke fuskantar koma-baya sakamakon yawan sace-sacen dalibai da ayyukan ’yan bindiga. Hakan na shafar ilimin ’ya’yanmu matuka, musamman mata,” inji shi.