Kotu ta tsare wasu mutane biyu a kurkuku kan zargin su da laifin satar ayaba da kudinta ya kai N10,000.
Kotun Majistare da ke Badagry a Jihar Legas ta bayar da umarnin tsare su ne a kurkukun Awhajigoh, bayan sun amsa laifuka biyu da suka shafi sata.
Alkalin kotun, NA Layeni ya kuma dage ci gaba da sauraren karar har zuwa ranar 24 ga watan Janairu domin yanke hukunci.
Tun da farko, dan sanda mai gabatar da kara, ASP Clement Okuoimose, ya shaida wa kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 6 ga watan Janairu inda suka hada baki da dare suka aikata laifin.
ASP Okuoimose ya ce wanda ake tuhumar ya saci tarin agada da ayaba da kudinsu ya kai N10,000 mallakin wata mai karar Alhaja Bilikisu.
Hakan a cewarsa, laifi ne a karkashin sashe na 411 da 287 na dokar laifuka ta jihar Legas, 2015.