✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Sata muke yi da karuwanci mu samu kudin shaye-shaye a Sabon Gari’

Bincike ya nuna akwai daruruwan irin wadannan yaran da ke gararamba a Sabon Gari.

  • Talauci, sakacin iyaye da mugayen abokai ne ummul-aba’isu – Gidauniya
  • Dole kowa ya ba da gudunmawa kafin a yaki matsalar – Masani

“Na fara shaye-shaye shekara uku da suka gabata, lokacin da wani abokina ya koya min. na kan sha sigari da sholisho da kuma giya. Tsawon wannan lokacin, a unguwar Sabon Gari nake zaune. Gaskiya rabona ma da ganin iyayena, wadanda ke unguwar Dorayi, tun da na bar gida a wancan lokacin. Ba su ma san ina nan ba. Kullum sai na yi sata nake samun abin da zan ci.”

Wadannan sune kalaman Gambo Sabo, wani yaro mai kimanin shekara 16 da haihuwa da ya tsunduma harkar shaye-shaye, wanda ke gararamba a unguwar Sabon Gari da ke Kano, bayan ya fara shaye-shayen tun yana shekara 13 a duniya.

Jikin matashin dai na nuni da cewa akwai yiwuwar ya shafe tsawon lokaci jikinsa bai taba ruwan wanka ba, ballantana a yi maganar yin sallah.

Labarinsa daya ne daga cikin na sauran daruruwan yaran da suka gudu suka bar gidajen iyayensu suka tsunduma harkar shaye-shayen, suna kwana a sararin Allah Ta’ala, sannan suke dogaro da sata da sauran laifuka domin tafiyar da rayuwarsu.

Binciken da Aminiya ta gudanar ya gano cewa akasarin irin wadanna matasa yara ne, wadanda shekarunsu ba su wuce tsakanin 10 zuwa 20 ba.

A cewar Gambo Sabo, ya bar gidan iyayensa da ke unguwar Dorayi a cikin birnin Kano shekara uku baya ne lokacin da ya saci wasu kudade a gidan, wadanda yawansu ya haura N200,000, sannan wani abokinsa ya ba shi shawarar ya sayi kayan maye ya fara jarrabawa.

Ya ce tun daga nan ya ci gaba da shaye-shaye, har zuwa lokacin da ya bar gaban iyayensa dungurungum, ya tare a Sabon Gari, inda yanzu yake rayuwa cikin ’yan uwansa mashaya.

Da Aminiya ta tambaye shi ko iyayen nasa ko kuma wani daga cikin danginsa sun san yana unguwar ko kuma halin da yake ciki tun bayan barinsa gida, sai ya ce bai taba haduwa da ko da mutum daya daga cikinsu ba, ko da a kuskure, kasancewar ba su ma san yana cikin birnin Kano ba.

“Mu kan kwana a waje a karkashin wata fafarandar kofar shagunan mutane da daddare, da rana kuma muka fita mu yi sace-sace don samun kudin abinci da na sayen kayan shaye-shayen.

“Kafin na baro gida, na kai kusan izu 40 a Alkur’ani, kanena ma ya yi sauka.

“Na taba jin ance wai kishiyar mahaifiyarmu ce ta yi min asiri saboda in shiga duniya, a nesanta ni daga gida. Amma Allah ma Ya sani ba abin da rasa a gida a lokacin, kawai sharrin Shaidan ne. Ina fatan wata rana Allah Ya shirye ni in daina,” inji shi.

‘A wajen tallan fiya wota aka koya min’

Shi ma wani mashayin, Amadu Dantala, ya ce ya shafe tsawon shekara 10 yana shaye-shayen, kuma an koya masa ne lokacin da yake tallan ruwan leda, wato ‘fiya wota’ a Sabon Gari.

“Ina cikin tallan fiya wota ne a nan wajen titin Church Road a Sabon Gari, sai daya daga cikin masu sayen ruwan ya ba ni shawara nima na saya na jarraba don inji abinda suke ji, to tun daga nan na fara kuma na ci gaba, ga shi har na shekara 10.

Ga Abdullahi Tanko, wanda dan asalin unguwar Zangon Dakata ne, ya ce ya shafe shekara biyar yana shaye-shayen, kuma yana samun kudin sayen kwayoyin ne daga sana’arsa ta gwangwan.

“Na koyi shaye-shaye ne daga abokaina. Na fara tun ina fafe kara in sha, lokacin ma ba zan iya sayen sigari ba, har ta kai ina iya sayen sigarin da ake kira da Super King ta N5 daga bisani. Ina samun kudin shaye-shayen ne daga sana’ar danben da nake yi,” inji Lawal Sanda, wani mai shaye-shayen shi ma a Sabon Garin.

Sai dai kusan dukkan masu shaye-shayen da suka zanta da Aminiya sun bayyana aniyarsu ta dainawa wata rana.

Mata ma ba a bar su a baya ba

Binciken na Aminiya ya gano cewa ba iya maza ne kawai ke ta’ammali da kayan shaye-shayen a unguwar ta Sabon Gari ba, mata ma ba a barsu a baya ba.

Wasu daga cikinsu sun ce sun dogara ne da karuwanci wajen sayen kayen mayen da kuma ciyar da kansu, yayin da su ma suke kwana a kofar shagunan Sabon Garin.

Aisha Gambo, wata budurwa wacce ta ce ’yar asalin unguwar Tudun Murtala ce a Kano, ta ce ta fara shaye-shaye ne kimanin shekara bakawai da suka wuce sakamakon wata matsala da ta fuskanta da wasu daga cikin ’yan uwanta.

“Kawayena su kan aike ni na sayo musu kayan maye, to a sakamakon haka, da kuma matsalolin da nake fuskanta a gidan, na fara shaye-shayen.

“Ina shan sigari da sholisho da kuma giya. Mu kan kwana a kofar shagunan mutane da daddare, sannan mu kan kwanta da maza don samun kudin abinci,” inji ta.

Talauci da sakacin iyaye da mugayen abokai ne ummul-aba’isu – YAFODA

A cewar wata gidauniya mai zaman kanta wacce ke rajin wayar da kan masu shaye-shaye (YAFODA) ta kan tallafa wa irin wadannan mashayan ta hanyar shirya musu bitoci da raba musu abinci da kuma sutturu da kuma sada wasu daga cikinsu da iyayensu.

A cewar Shugaban gidauniyar, Abubakar Shu’aibu Maitumaki, tabarbarewar tarbiyya daga gidaje da talauci da kuma sakacin iyaye na taka muhimmiyar rawa wajen jefa yaran cikin harkar.

“Binciken da muka gudanar da kuma alkaluman da muka tattara sun nuna cewa a kwai irin wadannan matasan kimanin 1,000 da ke gararamba a titunan Sabon Gari, amma ba mu da karfin daukar nauyin kula da su duka.

“Nan wajen kamar sansaninsu ne, duk wanda ya gagara nan yake tahowa.”

‘Akwai mummunar illar da take tunkararmu a nan gaba’

Abubakar Maitumaki ya kuma ce, “Wadannan yaran ba karamar barazana suke da ita ba, matukar ba a tashi tsaye an yi wani abu a kansu ba.

A zahirin gaskiya, hatta matsalolin tsaron da muke fuskanta a yanzu na tsaro na da nasaba da shaye-shayen miyagun kwayoyi.

“La’akari da haka, wannan gidauniya ta sada kusan mashaya 400 da iyayensu.

“Mun samu nasarar kai su jihohinsu daban-daban guda 14, sai kuma wasu daga ciki da muka kai Jamhuriyar Nijar,” inji Maitumaki.

Ya kuma ce yanzu haka gidauniyar na yunkurin ganin ta gina cibiyar gyaran hali ga masu shaye-shayen, yana mai kira ga sauran kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu hannu da shuni da su tallafa musu domin su kai ga gaci.

Sakacin iyaye da mugayen abokai da yawaitar kwayoyin na taka muhimmiyar rawa – Masani

Dokta Maikano Madaki, malami a sashen Nazarin Halayyar Dan Adam na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK), ya ce akwai dalilai na tattalin arziki da na tarbiyya da kuma na dabi’a da suke taka muhimmiyar rawa wajen jefa yara masu karancin shekaru a harkar shaye-shayen.

A cewarsa, “Sakacin iyaye wajen tarbiyyantar da ’ya’ya na taka muhimmiyar rawa kasancewar iyaye sune makaranta ta farko ga yaro.

“Sannan akwai batun bazuwar kwayoyin a ko ina, ta yadda ake samunsu ba tare da wata wahala ba, sai kuma talauci.

“Kazalika, akwai ciwon matsananciyar damuwa da ake kira da ‘depression’ a Turance, ko da yake tasirinsa bai kai na sauran dalilan ba, amma in ya hadu da mugayen abokai sai ya yi tasiri.

“Daga karshe akwai batun son jin abin da ake ji. Mutane su kan so su ji me masu shaye-shaye ke ji in suka sha, to da zarar an ba su sun dandana, sai su ci gaba,” inji malamin.

Dangane da hanyoyin da ya kamata a bi wajen kawo karshen matsalar, masanin ya ba da shawarar a sake duba yanayin aure da tarbiyyar ’ya’ya, saboda a cewarsa, nan ne tushe.

Ya kuma ba iyaye shawarar su rika tantance da wa ’ya’yansu ke yin abota tare da yin kira ga kungiyoyi masu zaman kansu a dukkan yankuna su shigo don ba da tasu gudunmawar.

“Daga karshe kuma, akwai bukatar hukumomin gwamnati da aka dora wa alhakin yaki da shaye-shayen su dada matsa kaimi wajen hana sarrafawa, rarrabawa, sayarwa da kuma shan miyagun kwayoyin. A nan, gwamnati ce kadai za ta iya shigowa.

 

A LURA: Dukkan sunayen masu shaye-shayen da aka yi amfani da su a cikin labarin nan ba sunayensu ba ne na asali. An boye su ne saboda karancin shekarunsu.