Sarkin Zazzau, Ahmad Nuhu Bamalli, ya bukaci limaman addinai da ke masarautarsa su fara gudanar da addu’o’i na musamman domin samun tsaro da zaman lafiya a yankin da ma Najeriya baki daya.
Sarkin Zazzau, ta wata sanarwa da ya fitar ta bakin jami’in yada labaransa, Abdullahi Aliyu, ya ce gudanar da addu’o’in ya zama wajibi, ganin yadda ’yan bindiga ke ci gaba da yi wa mutanen masarautar kisan gilla.
- An damke masu yi wa ’yan bindiga safarar karuwai
- Ba za mu karbi tubar ’yan bindiga ba, kashe su za mu yi —El-Rufai
Ya yi kira ga Musulmi da su yi amfani da kiran nasa wajen gudanar da addu’o’i a lokacin salloli biyar na farilla, Kiristoci kuma a lokacin ibadarsu.
Da yake jajantawa ga iyalan wadanda aka kashe a harin, Sarkin Zazzau, ya kuma yi addu’ar samun sauki ga wadanda suka samu raunuka a hare-haren.
Hare-haren baya-bayan a yankin Masarautar Zazzau sun sa sarkin ya dakatar da wasu tafiye-tafiyensa.