Sarkin Zazzau Ahmed Nuhu Bamalli, ya kai wa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ziyara ta farko ga Gidan Gwamnatin Jihar Kaduna.
Ziyarar da sarkin ya jagoranci ‘yan Majalisar Masarautar Zazzau na zuwa ne mako guda bayan Gwamnan ya nada shi Sarkin Zazzau na 19.
- Iyan Zazzau ya nemi kotu ta soke nadin Bamalli
- Tirka-tirkar da aka yi kan nada Sarkin Zazzau
- Sarkin Zazzau: Masu Zaben Sarki sun yi mubaya’a
A ranar Laraba 7 ga Oktoba, 2020 ne Gwamnatin Jihar Kaduna ta nada Sarki Ahmed Bamalli bayan rasuwar Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris sakamakon rashin lafiya.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta kawo muku rahoto cewa daya daga cikin wadanda suka nemi kujerar mulkin, Iyan Zazzau Alhaji Bashar Aminu, ya shigar da kara yana kalubalantar nadin sarkin.
Iyan Zazzau wanda shi ne ya fi samun kuri’u daga cikin wadanda masu zabar sarki na masarautar suka zaba na bukatar kotu ta dakatar da ba wa Sarki Ahmed Sandar Mulki ta kuma ayyana sarautar da aka ba shi a matsayin haramtacce.
Karar da ya shigar a gaban Babbar Kotun Jihar Kaduna na bukatar a ayyana Alhaji Bashar Aminu a matsayin halastaccen Sarkin Zazzau na 19 kasancewarsa wanda ya fi samun kuri’u a zaben da aka yi.