✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Saudiyya ya nada dansa a matsayin Fira Minista

Sarki Salman ya yi sauye-sauye a Majalisar Ministocinsa tare da nada dansa a Fira Minista, mukami da da bisa al’ada sarkin ne ke rikewa

Yarima Mai Jiran Gado na Saudiyya, Mohammed ibn Salman, ya zama sabon Fira Ministan kasar.

Sanarwar da Masarautar Saudiyya ta fitar ta ce Sarki Salman bin Abdelaziz ne ya nada dan nasa a mukamin, wanda da bisa al’ada sarkin ne ke rike da shi.

Sai dai sanarwar wadda kamfanin yada labaran kasar ya wallafa, ta bayyana cewa Sarki Salman ne zai rika jagorantar duk zaman majalisar da ya halarta.

Sabuwar dokar ta bayyana wasu sauye-sauye a majalisar ministocin kasar, inda aka nada dan uwan sabon Fira Ministan, Yarima Khalid bin Salman a matsayin Ministan Tsaro.

Yousef bin Abdullah bin Muhammad al-Bunyan shi ne sabon Ministan Ilimi, Yarima Faisal bin Farhan a matsayin Ministan Harkokin Waje, sai Khalid bin Abdulaziz al-Falih a matsayin Ministan Zuba Jari.

Yarima Abdulaziz bin Salman zai ci gaba da rike mukaminsa na Ministan Makamashi.

Shi ma Yarima Abdulaziz bin Saud bin Nayef bin Abdulaziz zai ci gaba da rike mukamin Ministan Harkokin Cikin Gida.

Haka kuma Mohammed bin Abdulahi al-Jadaan kuma zai ci gaba da rike mukamin Ministan Kudi.