✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Saudiyya ya bukaci a yi Sallar Rokon Ruwa

Sarki Salman bin Abdulaziz ya bukaci a koma ga Allah, a tuba, sannan a yawaita ayyukan alheri

Sarki Salman bin Abdulaziz na  Saudiyya ya umarci limaman kasar da su jagoranci gudanar da Sallar Rokon Ruwa.

A umarnin da Sarki Salman ya bayar ranar Juma’a, ya ce za a gudanar da Sallar Rokon Ruwan ce a ranar Litinin, 9 Jumada ga watan Al Awwal 1443 bayan hijira.

Ya kuma bukaci al’ummar kasar da cewa “Kowa ya yawaita neman gafara da tuba zuwa ga Allah, ya nemi kusanci ga Allah;

“A yawaita ayyuka na gari da kuma nafiloli kamar bayar da sadaka da taimakon mabukata da kuma ambaton Allah.

“Muna fata da wadannan ayyukan Allah zai biya mana bukata Ya yaye mana halin da muka tsinci kanmu a ciki,” inji sakon Sarkin.