Shugaban Kungiyar Sarakunan Samari ta Najeriya Alhaji Uba Sani Daura ya yi kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da aikin ba sani ba sabo wajen tabbatar da zaman lafiya a fadin kasar musamman wuraren da suka yi kaurin suna wajen kai hare-hare na ba gaira ba dalili. Shugaban Kungiyar Sarakunan Samarin kuma Sarkin Samarin Daura da ke Jihar Katsina ya bayyana haka ne bayan kammala taron da suka gudanar a Kaduna a ranar Asabar da ta gabata.
“Muna amfani da wannan dama a matsayinmu na sarakunan samari daga jihohi daban-daban kasancewar akasarin jama’ar kasar nan matasa ne kuma su ne kashin bayan ci gaban kowace al’umma, lura da haka, tare da ganin irin halin da mafi yawan matasanmu ke ciki ta sanya muka shirya wannan taro tare da gayyato ’yan uwanmu daga sassan Najeriya don duba irin gudunmawar da za mu iya bayarwa. Mu ne mafi kusa da matasa don ganin sun shiga inda za a dama da su, don ba da tasu gudunmawar ga ci gaban kasa tare da rungumar ayyukan dogaro da kai don magance zaman banza da shaye-shaye da suka yi katutu a cikin al’ummarmu,” inji shi
Sai ya yi kira ga Shugaban Kasa ya yi dubi ga irin gudunmawar da sarakunan matasan Najeriya za su iya badawa tare da ba su cikakken goyon baya da hadin kai don a gudu tare a tsira tare.
“Ba mu da wata kasa da ta wuce Najeriya don haka a shirye muke mu bayar da tamu gudunmawar tare da hada kai da dukkan masu son kawo ci gaba a cikin kasa tare da yakar munanan dabi’un da suke addabar matasa da sauran jama’ar kasa,” inji shi.
Da yake yi wa Aminiya karin haske bayan kammala taron, Sarkin Samarin Jama’a a Jihar Kaduna kuma mai masaukin baki, Alhaji Mudi Shafi’u Tahir ya nuna godiyarsa kan yadda taron ya gudana cikin kwanciyar hankali tare da fahimtar juna inda ya ce wannan yunkuri ne da suka fara samar wa matasa mahanga mai kyau don samun kyakkyawar makoma ga kasar a gobe.
Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai sarakunan samari daga jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da Sakkwato da Oyo da Enugu da Adamawa da Bauchi da kuma Filato.