Bayan kwana guda da karbar tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II tare da Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna, a ranar Litinin, Mai Alfarm Sarkin Musulmi, ya kai wa gwamnan ta shi ziyarar.
Sarkin Musulmin Muhammad Sa’ad Abubakar KK ya sauka a Gidan Gwamnatin Kaduna na Sir Kashim Ibrahim da misalin karfe da azahar cikin wata bakar mota kirar Jeep.
Daga cikin tawagar da ta tarbi Sultan dan akwai Sakataren Gwamnatin Jihar, Balarabe Abbas; Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Jihar, Muhammad Sani Dattijo da kuma Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Samuel Aruwan.
Sai dai ya zuwa lokacin da aka tattaro wannan rahoto, manema labarai ba su iya gano abin da ganawar Sarkin Musulmin da Gwamnan za ta kunsa ba.
Aminiya ta ruwaito cewa, dubban mutane sun yi dandazo domin yi wa tsohon Sarkin Kano lale maraba yayin da ya ziyarci El-Rufai a ranar Lahadi.