Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya tabbatar da ganin jinjirin watan Zul-Hijjah a Najeriya, wanda hakan ya tabbatar da ranar Alhamis a matsayin ranar daya ga watan.
Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA) ya ce ranar dai ita ce ta yi daidai da 30 ga watan Yunin 2022.
- LABARAN AMINIYA: ’Yan Bindiga Sun Fara Harbin Fasinjojin Jirgin Kasan Da Ke Hannunsu
- Kotu ta yanke wa mawaki R-Kelly hukuncin shekara 30 a kurkuku
Hakan dai na nufin a bana za a yi bikin Sallah Babba ranar Asabar, tara ga watan Yulin 2022.
Watan Zul-Hijjah dai shi ne watan na 12 kuma na karshe a kalandar Musulunci, kuma a cikinshi ne Musulmai daga ko ina daga fadin duniya ke gudanar da Aikin Hajji a kasar Saudiyya.
Kazalika, yayin bikin Sallar, Musulmai kuma na gudanar da ibadar Layya, inda sukan yanka dabbobi domin raba naman ga ’yan uwa da mabukata.