✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ya ba da umarnin dubin watan Ramadan

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama'a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha'aban,…

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayar da umarni ga jama’a da su fara duban jaririn watan Ramadan daga ranar Jumu’a 29 ga watan Sha’aban, 1446 Bayan Hijira, wanda ya yi daidai da 28 ga watan Fabrairu, 2025.

Shugaban Kwamitin Bayar da Shawara kan Harkokin Addini a Fadar Sarkin Musulmi, Wazirin Sakkwato, Farfesa Sambo Wali Junaidu ne ya sanar da hakan a wata takarda da ya raba wa manema labara.

Wazirin Sakkwato ya ce duk wanda ya samu ganin jinjinrin watan Ramadan ya sanar da hakimi ko uban ƙasar da ke kusa da shi.

Daga nan ne za a kai maganar ga Sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar.

Ya roƙi Allah Ya taimake su a cikin wannan aikin da suke yi na addini.

Ramadan shi ne wata na tara a kalandar Musulunci, kuma al’ummar Musulmi na azumtar sa baki ɗaya.

Azumin Ramadan shi ne ka uku a cikin ginshikan addinin Musulunci guda biyar.