Majalisar Addinai ta Kasa (NIREC) ta bukaci gwamnatin tarayya da na jihohi su fallasa tare da hukunta masu daukar nauyin ayykan ta’addanci.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III tare Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN), Daniel Okoh ne suka yi kiran a wurin taron da suka gudanar a Abuja.
Shugabannin addinan sun koka bisa mummunar illar da ayyukan ’yan bindiga da dangoginsu ke yi wa al’ummomi, gami da raba jama’a da muhallansu da lalata rayuwarsu da kuma mayar da su ’yan gudun hijira a cikin kasarsu.
Sarkin Musulmi ya bukaci ’yan Nijeriya su koma ga Allah su nemi rahamarSa da dawowar zaman lafiya da ci-gaban kasar.
- Sanatocin Arewa sun nemi a janye kudurin dokar harajin Tinubu
- DAGA LARABA: Abin ya sa ’yan Nijeriya ke kishin ƙabila fiye da ƙasa
Sarkin Musulmi ya kuma gargadi ’yan siyasa da su ji tsoron Allah su guji tara dukiya ta hanyar haram da kuma mara amfani.
A nasa bangare, Archbishop Okoh, ya jaddada muhimmancin shugabanni su alkinta albarkatun da Allah Ya huwace wa Nijeriya domin amfanin jama’a, maimakon su mayar da su tushen rikice-rikice da kuma rashin tsaro.
Shugaban addinin ya kuma yi kira da a karfafa bangaren shari’ar Nijeriya domin yin adalci da kuma hukunta masu yin zagon kasa ga ci-gaban kasa da kuma sha’anin tsaro.
Sakataren NIREC, Rabaran Cornelius Omonokhua, ya koka kan yadda ake wasu tsiraru ke cin moriyar ma’adinan Nijeriya ta hanyoyin da ke cutar da ’yan kasar a yankunan Kudu da Arewa.