✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi ya ayyana ranar Laraba a matsayin Sallah

Ta tabbata ranar Laraba za a yi sallah ƙarama a Najeriya.

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Laraba a matsayin ranar Sallah a Najeriya.

Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya ce ranar za ta kasance 1 ga watan Shawwal na shekarar 1445, daidai da 10 ga watan Afrilu, 2024.

Hakan dai na nufin a bana za a yi bikin Sallah ranar Laraba, kuma za a yi azumi 30 a watan Ramadan.

Watan Ramadan dai shi ne watan na tara a kalandar Musulunci.

Kazalika, yayin bikin sallah, Musulmai na gudanar da addu’o’i da sauran bukukuwa domin sada zumunci da nuna kauna a tsakaninsu.