Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Laraba a matsayin ranar Sallah a Najeriya.
Sarkin, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (NSCIA), ya ce ranar za ta kasance 1 ga watan Shawwal na shekarar 1445, daidai da 10 ga watan Afrilu, 2024.
Hakan dai na nufin a bana za a yi bikin Sallah ranar Laraba, kuma za a yi azumi 30 a watan Ramadan.
Watan Ramadan dai shi ne watan na tara a kalandar Musulunci.
Kazalika, yayin bikin sallah, Musulmai na gudanar da addu’o’i da sauran bukukuwa domin sada zumunci da nuna kauna a tsakaninsu.