✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Musulmi bai mutu ba — Fadar Sarkin Musulmi

Fadar ta yi Allah-wadai da jita-jitar da musanta labarin, inda ta ce Mai martaba, Sa’ad Abubakar yana cikin ƙoshin lafiya.

Fadar Sarkin Musulmai a Nijeriya ta yi magana kan jita-jitar rasuwar Sarkin Musulmi da ake yaɗawa.

Fadar ta yi Allah-wadai da jita-jitar da musanta labarin, inda ta ce Mai martaba, Sa’ad Abubakar yana cikin ƙoshin lafiya.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Fadar Sarkin Musulmi, Aminu Haliru ne ya fitar da bayani, inda ya ce Masarautar Sarkin Musulmi ta yi watsi da maganar, duk da dai kowa ya san dukkan mutum zai mutu idan lokacin barin duniya ya zo.

Tun farko, Shugaba Ƙungiyar MPAC, Disu Kamor ya yi fatali da labarin da ake ta yaɗawa kan rasuwar mai Martaba. Kamor ya ce, lafiyar Sarkin Musulmi garau babu abin da yake damun sa a halin yanzu. Ƙungiyar ta gargaɗi al’umma da su guji yaɗa jita-jita da kuma tantance labari kafin fara yaɗawa.

Ta ce, irin waɗannan labarai marasa kan gado babu abin da za su ƙara illa rarrabuwar kawuna da kawo ruɗani.

Sa’in Kilgori, Dakta Muhammadu Jabbi Kilgori shi ya tabbatar Sarkin Musulmi na raye. “Ba mu san mene ne suke son cimmawa da wannan jita-jitar ba, amma tabbas Sarkin Musulmi yana cikin ƙoshin lafiya.”

Ɗazu ma muka bar Jihar Kaduna domin halartar wani taro a birnin Tarayya Abuja kamar yadda ya saba.”