Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya dakatar da Hakimin Kankara, Sarkin Pawwan Katsina, Alhaji Yusuf Lawal.
Sakatare Masarutar Katsina kuma Sarkin Yakin Katsina, Alhaji Mamman Ifo ya ce an dakatar da Hakimin Kankara ne bisa zargin sa da alaka da ayyukan ’yan sa-kai da ake zargi da miyagun ayyuka a yankin.
- ’Yan Boko Haram na farautar malamai a Geidam
- Hattara dai mata: Mu yi wa kanmu fada kafin ranar da-na-sani
- Babu ranar dawowar albashin N30,000 a Kano
Sarkin Yakin Katsinan ya yi watsi da bayanan da ke cewa kage aka yi wa basaraken wajen danganta shi da ’yan sa-kan da a baya suka rika cin karensu babu babbaka.
Ya ce dakatarwar na daga cikin matakan da Masarautar ta dauka na tabbatar da goyon bayanta ga Gwamnatin Jihar wajen yaki da ayyukan ta’addanci.
A cewarsa, Masarautar da riga ta kafa kwamiti na musamman domin gudanar da bincike a kan Hakimin na Kankara.
Sai dai ya ce babu zargin alaka da ’yan bindiga a kan basaraken, amma jami’an tsaro da al’ummar Kankara na korafin a kansa, shi ya sa ake bincike game da zarge-zargen.
Ya kara da cewar bayan kammala binciken, kwamitin zai mika rahotonsa ga gwamnatin jihar, kuma idan ba a same shi da laifi ba, za a dawo da shi kan kujerarsa.
Sai dai ba a bayyana hakikanin ayyukan ’yan sa-kan da ake zargin basaraken da hannu a ciki ba.