Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya dawo da Alhaji Aminu Babba Danagundi kan sarautarsa ta Sarkin Dawaki, tare da yi wa sarautar kwaswarima ta koma Sarkin Dawaki Babba.
Sarkin Kanon ya bayyana haka ne a wata takarda da Masarautar Kano ta aike zuwa Ofishin Sakataren Gwamnatin Jihar Kano Alhaji Usman Alhaji, dauke da sa hannun Dan Rimin Kano Alhaji Sarki Waziri, don neman sahalewar gwamnatin jihar.
Da yake tabbatar da hakan mai magana da yawun Sakataren Gwamnatin Uba Abdullahi ya ce sakataren ya karbi takardar tun ranar 8 ga watan Yuli ya kuma mika ta ga ofishin Gwamna.
Idan za a iya tunawa a shekarar 2003 ne Masarautar Kano ta tunbuke Alhaji Aminu Danagundi daga kujerarsa.
A baya-bayan nan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin cirewar da aka yi masa.
Amma sai ga shi wannan sarkin ya yi mi’ara koma baya ga matakin da mahaifinsa ya dauka a na tube basaraken.
A wani makamacin wannan, Sarkin Kanon ya nada wansa Alhaji Sanusi Ado Bayero a matsayin Wamban Kano.
Alhaji Sanusi shi ne tsohon Ciroman Kano a zamanin mulkin mahaifinsa Alhaji Ado Bayero.