Sarkin Jama’a da ke Kudancin Jihar Kaduna, Muhammadu Isa Muhammadu, ya yi kira ga al’ummar masarautarsa da su ci gaba da zama lafiya tare da girmama juna don samun ci gaba a masarautar da ma Jihar Kaduna baki daya.
Sarkin ya yi wannan kiran ne a wajen walimar buda-baki da ya saba shiryawa a fadarsa a duk shekara, inda Musulmi da Kiristoci ke halarta tare da sauran masu ruwa da tsaki daga ciki da wajen garin don yaukaka dankon zumunci a tsakaninsu.
- Shekara 68 da kafa Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya
- An kama masu zanga-zanga kan yunkurin kone Alkur’ani a Sweden
Sarkin ya kuma jinjinawa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi wajen dakile duk wata matsala a lokacin da ake bukatar su cikin gaggawa.
Da yake jawabinsa tun da farko, Kuyambanan Jama’a, Alhaji Garba Abdullahi Maisukuni, ya ce Sarkin kan yi amfani da wannan dama a kowane watan Ramadan ne don tattaro mabiya addinai daban-daban daga mabambantan kabilu don cin abinci tare da yin addu’o’i tare don samun hadin kai da fahimtar juna.
Da suke jawabi, wakilin Kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNA) Alhaji Iliyasu Musa Kalla, da takwaransa na Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) Rabaran Ben Thomas Ayuba da sun yaba wa sarkin bisa yadda yake bayar da hadin kai tare da taimaka wa shugabannin addinai wajen magance matsaloli idan sun taso.
Sannan sun bayyana takaicinsu kan yadda wasu matasan Musulmi da Kirista marasa zuwa mallaci ko coci amma su ne kan gaba wajen hada fitina.
Shugabannin kungiyoyin addinan sun bukaci a rika kulawa da irin wadannan matasan a kowace irin al’umma domin barazanarsu na da hatsari.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Kwamred Yunana Markus Barde ya jinjina wa sarkin da yake sadaukar da komai nasa don ganin an zauna lafiya.
Ya ce Gwamnatin Jihar Kaduna ta tashi haikan wajen ganin ta maido da jihar kan turbar zaman lafiya don samun cigaba mai ma’ana wanda hakan zai yiwu ne kawai idan ta magance mummunan halin da ake ciki.
Sannan a karshe ya roki kowa da ya rungumi dan uwansa don zama lafiya ba tare da nuna banbancin kabila ko addini ko na jam’iyyar siyasa ba.