✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Hausawan Ibadan ya zama ‘mamba’ a Majalisar Sarakunan Yarbawa

An yi hakan ne don a samu saukin isar da sakon masarautar da jama’arsa.

Majalisar Sarakunan Karamar Hukumar Ibadan ta Arewa a Jihar Oyo ta sa sunan Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Dahiru Zungeru a matsayin mamba da zai rika halartar taron majalisar da ta saba yi a kowane wata.

Manyan masu rike da sarautu a fadar Olubadan, Osi-Olubadan Cif Lateef Gbadamosi Adebimpe da Ekefa-Balogun na Olubadan Cif Sharafadeen Alli ne suka shugabanci zaman majalisar da ta amince da sa Sarkin Hausawan a cikin majalisar tasu.

A wajen taron sarakunan sun yi bayanan da suka shafi hadin kan al’ummomin Najeriya da suke zaune a Masarautar Ibadan da lalubo hanyar bunkasa tattalin arziki a Jihar Oyo da batun tsaron kasa baki daya.

A jawabinsa a wajen taron Osi-Olubadan Cif Lateef Gbadamosi Adebimpe ya ce, majalisar ta amince da janyo Sarkin Hausawan cikinta ne domin ya kasance jagoran isar da sakon fadar Olubadan da Gwamnati ga jama’arsa.

Kuma Sarkin zai samu saukin isar da sakon jama’arsa ga mahukunta ta wannan hanya.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Oyo, Ekefa-Balogun Cif Sharafadeen Alli ya ce, “Wannan ranar farin ciki ce ga dukkan al’ummar Yarbawa da Hausawa da suke zaune a Masarautar Ibadan kan amincewa a sanya Sarkin Hausawan a cikin majalisar, wanda hakan wata dama ce ta kyautata zamantakewa da hadin kan kasa.”

Da yake nuna farin cikinsa kan daukaka martabarsa Sarkin Hausawan Ibadan, Alhaji Ali Dahiru Zungeru wanda yake tare da manyan hakimansa, ya ce, “Babu abin da zan fada a nan sai godiya ga Allah da Ya kawo mu ga wannan matsayi. Mun yi alkawarin yin adalci wajen tafiyar da mulki tsakani da Allah don samar da kyakkyawan hadin kai a tsakanin jama’ata da jama’ar gari Yarbawa don a samu dunkulalliyar Najeriya.”

Sarkin Hausawan ya yi kira ga jama’arsa su tashi tsaye wajen lalubo ayyuka da sana’o’in dogaro da kai domin kauce wa wulakanci.

Kansila a Sashin Dokoki na Karamar Hukumar Ibadan, Alhaji Ibrahim Faira cewa ya yi, “Wannan matakin farko ne da muka fara dauka wajen ganin sunan Sarkin Hausawan ya shiga cikin majalisar domin a yi tafiya tare da mu.

“Saboda haka muke neman mutanenmu su taimaka wa Sarkin ta fannin bayar da goyon baya da hadin kai da girmama doka da oda domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a wannan sashe da kasa baki daya.