✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarkin Hausawan Ibadan ya kwanta dama

Za a yi jana'iza ranar Litinin bayan Azahar.

Sarkin Hausawan Ibadan Alhaji Ahmad Dahiru Zungeru ya riga mu gidan gaskiya.

Da misalin karfe 9 na daren ranar Lahadi ne Sarkin ya rasu a gidansa da ke unguwar Sabo da ke birnin Ibadan bayan gajeruwar rashin lafiya.

Majalisar Masarautar Hausawan Ibadan mai kunshe da Hakimai fiye da 50 ta tabbatar da rasuwar Sarkin, wanda ya shekara 29 a kan karagar mulki.

Ta kuma fara shirye-shiryen jana’izar marigayin da za a gudanar a ranar Litinin da misalin karfe 2 na rana.

Tuni dai aka kafa kwamitoci da aka dora wa alhakin sanar da rasuwar ga Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde da Mai Martaba Olubadan na Ibadan Oba Saliu Adetunji da Sarkin Musulmin Yarbawa da Babban Limamin Ibadan Sheikh Abdulganiyu Abubakar Agbotomokekere da kuma kusoshin jam’iyun siyasa da makamantansu game da shirye-shiryen jana’izar.

Marigayi Alhaji Ahmadu Dahiru Zungeru mai shekara 76 an nada shi Sarkin Hausawan Ibadan ne a ranar 13 ga watan Fabrairu, 1992.