Sarkin Hadeja, Dokta Adamu Abubakar ya bukaci masu fada a ji na kasar nan da su kara tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta rutsa da su a Jihar Jigawa.
Sarkin ya bayyana hakan ne yayin da yake karbar bakuncin gwamnan jihar, Muhammad Badaru Abubakar da dan takarar shugaban kasa na jam’iyar APC a 2023 Bola Tinubu, a ziyarar jajen ambaliyar da suka kai masa.
Tinubu ya mika masa tallafin Naira miliyan 50, don raba ga wadanda ibtila`in ya rutsa da su a jihar Jigawa.
Ya ce a matsayinsa na shugaban majalisar sarakunan jihar, zai tattauna da sauran sarakuna hudun, kan yada za a yi rabon tallafin.
“Wadannan kudi za su isa ga wadanda ibtila’in ya shafa kuma muna kira ga saurann masu fada a ji a Najeriya da su kara tallafa wa mutanen nan, domin suna cikin mawuyacin hali.
A baya dai Sakataren Zartaswa na hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar (SEMA), Sani Yusuf, ya ce ambaliyar ta yi sandiyar rushewar daruruwan gidaje da mutuwar mutane 50.
Ya ce hakan ya sanya mutanen da ambaliyar ta shafa tarewa a gine-ginen gwamnati, baya ga mutanen da gwamnatin jihar ta kafawa wani sansanin wucin gadi.
Da dama daga wadanda ambaliyar ta rutsa da su dai sun fito ne daga kauyen Balangu, inda mutane hudu suka mutu, gidaje akalla 237 kuma suka rushe.