✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarkin Daura ya rasa dan uwansa a hatsarin mota

Dan uwan Sarkin Dauran ya rasu ne tare da wasu abokansa biyu yayin da hadarin ya ritsa da su a kauyen Muduru.

Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruk Umar, ya rasa dan uwansa Alhaji Abdullahi Umar Maitaro yana da shekaru 56 da haihuwa.

Marigayin ya rasu ne tare da abokansa biyu a hatsarin mota a kauyen Muduru, dake kan hanyar Katsina zuwa Daura ranar Talata.

Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa, ya ce hatsarin ya faru ne bayan motar da suke ciki ta yi kokarin kaucewa babur mai kafa uku, a daidai lokacin da ya afkwa mata.

Nan take dai uku daga cikin mutum hudu dake cikin motar suka rasu, yayin da dayan kuma yake ci gaba da samun kulawa a asibiti.

Tuni dai Gwamnan jihar ta Katsina, Aminu Bello Masari, ya samu rakiyar mai ba shi shawara kan Ilimin Manya, Dakta Bashir Ruwangodiya, da sauran jami’an gwamnati don jajantawa Sarkin na Daura.

Har wa yau, gwamnan ya ziyarci gidan iyalan ragowar biyun da suka rasu, inda su ma ya yi musu ta’aziyya.