Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya naɗa Alhaji Munir Sanusi Bayero a matsayin sabon Galadiman Kano, tare da wasu manyan muƙamai guda huɗu.
Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Alhaji Kabir Tijjani Hashim, Hakimin Nassarawa, wanda ya zama sabon Wamban Kano; Alhaji Mahmud Ado Bayero Hakimin Gwale, wanda aka naɗa a matsayin Turakin Kano; Adam Lamido Sanusi a matsayin Tafidan Kano; da Alhaji Ahmad Abbas Sanusi a matsayin Yariman Kano.
- Ra’ayin Jama’a kan ziyarar Tinubu Katsina
- Gobarar rumbum makamai Maiduguri da Matakan da ya kamata a ɗauka — Ƙwararru
Da yake jawabi yayin bikin naɗin sarautar, Sarki Sanusi ya buƙaci sabbin masu riƙe da muƙaman da su kasance masu koyi da shugabanni da kuma ci gaba da kare martabar sarautar, tawali’u da tausayi ga jama’a.
“An zaɓo ku ne bisa la’akari da tarihinku da na iyalan ku, mafi yawanku kun nuna biyayyar ku ga Masarautu da zuriyarmu kuma kun bayar da gudunmawa sosai wajen tallafa wa talakawa da ci gaban al’umma, ina roƙonku da ku yi koyi da magabatanku, Allah Ya yi muku jagora wajen gudanar da ayyukanku,” in ji shi.
Taron wanda ya gudana a fadar Sarkin ranar Juma’a ya samu halartar Gwamna Abba Kabir Yusuf da ’yan majalisar zartarwa na jiha da shugabannin gargajiya da na addini da ’yan uwa da sauran masu faɗa a ji.
A wani lamari makamancin haka, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, shi ma ya naɗa Alhaji Sunusi Lamido Ado Bayero a matsayin Galadiman Kano a ƙaramar fadar Nassarawa.