✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarki Sanusi II ya yi Hawan Sallah a Birnin Dabo

Sarki Sanusi ya yi duk zagayen Hawan Sallah da bisa al’ada aka saba a Birnin Dabo.

Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II ya yi Hawan Sallah kamar yadda bisa al’ada aka saba gudanarwa a Birnin Dabo.

Kamar yadda al’ada ta tanada, Sarkin haye a kan doki ya ratso ta Kofar Wambai zuwa Zage zuwa ’Yan Damadan zuwa Shahuci sannan daga nan ya koma fada.

Sai dai a Hawan Sallar na yau, Sarkin ne kaɗai ya hau doki yayin da sauran masu riƙe da sarauta ke tafe a ƙafa wasunsu kuma a cikin motoci.

Daga nan sarkin ya tsaya a Gidan Shettima domin karɓar gaisuwar barka da sallah daga wurin Gwamna sannan ya ƙarasa fada, inda ya gabatar da jawabai gabanin komawarsa gida.

Aminiya ta ruwaito cewa, Sarki Sanusi ya yi Hawan Sallar ne bayan ya jagoranci Sallar Idi a Masallacin Juma’a da ke Ƙofar Mata.

An dai yi sallar ta bana ce a Masallacin Juma’ar na Ƙofar Mata a madadin filin Masallacin Idin a dalilin ruwan sama da ya malale farfajiyarsa.

Gwamna Abba Kabir Yusuf da sauran makarraban gwamnatinsa sun halarci Sallar Idin tare da Sarkin.

Aminiya ta lura cewa an yi sallar ta bana cikin matakan tsaro yayin da jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji, sibil difens suka yi dako wuri-wuri cikin shirin ko ta kwana.

Ana iya tuna cewa, a bayan nan ne rundunar ’yan sandan Kano ta haramta duk wasu haye-hayen sallah a bana bayan wani taron masu ruwa da tsaki kan tsaro da ta gudanar.

Sai dai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rashin jin daɗinsa kan wannan riga malam shiga masallaci da rundunar ’yan sandan ta yi ba tare da tuntubarsa ba.

Gwamnatin Kano ta ce hurumin gwamnan jihar ne ya ayyana ko za a yi hawan sallah ko akasin haka kasancewarsa lamba ɗaya a kula da harkokin tsaron jihar.

Gwamnatin ta kara da cewa abin takaici ne wasu su rika yin shishshigi a kan ikon da gwamna yake da shi don cimma wata manufa.

Rahotanni sun ce, Sarki Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya yi tasa sallar Idin ce a karamar fada da ke Nassarawa.

Ana dai ci gaba da taƙaddama kan sarautar Kano tsakanin Sarki Sanusi da Sarki Bayero, a yayin da ake dakon hukuncin da kotu za ta yanke kan rushe masarautun Kano huɗu da gwamnatin da ta gabata ta ƙirƙiro.