Sarki Salman Bin Abdulaziz na Kasar Saudiyya, ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari ta’aziyyar mutuwar Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru.
Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun Shugaba Kasar, Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ta ce Sarkin ya yi ta’aziyyar ne yayin da ya kira Shugaba Buhari ta wayar tarho a ranar Litinin.
Malam Shehu ya ce, Sarki Salman ya kuma taya kasar juyayi bisa wannan mummunan yanayi da ta tsinci kanta a ciki sanadiyyar rasuwar Babban Hafsan Sojin Kasar.
Kazalika, Shugaba Buhari da Sarkin sun yi musayar gaisuwar Idin Karamar Sallah da ta wakana makonni kadan bayan an kwashe kwanaki talatin ana Azumin watan Ramadana.
Sanarwar ta ce, “Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya yi wata ganawa ta wayar tarho da Sarki kuma Shugaban Masu Kula da Masallatai biyu na Harami, Sarki Salman bin Abdulaziz.
“Sarkin ya jajantawa Shugaba Buhari da jama’ar Najeriya dangane da hatsarin jirgin saman da ya yi ajalin Babban Hafsan Sojin Kasan Najeriya da kuma wasu hafsoshin soji goma.
“Sarkin ya kuma yi addu’ar Allah Ya jikan rayukan sojojin da suka riga mu gidan gaskiya.
“Shugaba Buhari ya bayyana farin cikinsa da kuma godiya ga wannan karamci na Sarki Salman gami da goyon bayan da ya ke yi wa Najeriya.”
Aminiya ta ruwaito cewa, a Juma’ar da ta gabata ce Allah Ya yi wa Babban Hafsan Sojin Kasan rasuwa sakamakon wani hatsarin jirgin sama da rutsa da shi a Jihar Kaduna.