✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sarki Bamalli ya rushe Majalisar Masarautar Zazzau

Nan da nan Tafidan Dawakin Zazzau ya mika takardar murabus dinsa.

Mai Martaba Sarkin Zazzau, Mallam Ahmed Nuhu Bamalli, ya sanar da rushe Majalisar Masarautar Zazzau a ranar Talata.

Hakan na zuwa ne bayan da sarkin ya sanar da cewa zai yi sauye-sauye a masarautar yayin jawabin shi na cika shekara daya a kan karagar mulki.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sakataren Masarautar, Alhaji Barau Aliyu ce ta bayyana hakan ba tare da wani karin bayani ba.

Wakilinmu ya ruwaito cewa sanarwar ba ta bayyana sunayen wadanda rushe Majalisar Masarautar ta shafa ba.

Bayanai sun ce tun a ranar Litinin masarautar ta ba da sanarwar nadin sabon Wazirin Zazzau, bayan shafe watanni wanda ke kai yana hutun dole.

Sanarwar da Alhaji Barau Aliyu ya fitar ta ce an sauke tsohon Wazirin, Alhaji Ibrahim Aminu, tare da nadin Khadi Mohammed Inuwa Aminu a matsayin sabon Waziri

Aminiya ta ruwaito cewa, jim kadan bayan fitar da wannan sanarwa ce Tafidan Dawakin Zazzau, Alhaji Shehu Iya Saidu, ya mika takardar murabus dinsa.

Kazalika, Masarautar Zazzau ta sake sanar da nadin Ambasada Suleiman Dauda Umar a matsayin sabon Turakin Dawaki.