Sarki Abdallah na kasar Jordan ya rantsar da sabuwar gwamnatin kasar a wani mataki na farfado da tattalin arzikin kasar da ke cikin matsi.
Yayin bikin da ya gudana a ranar Litinin, Sarkin ya umarci sabuwar gwamnatin karkashin Bisher al Khaswaneh ta hanzarta aiwatar sauye-sauyen da suka samu goyon bayan Asusun Lamuni na Duniya (IMF).
- Kotu ta yanke wa Donald Trump da Sarki Salman hukuncin kisa
- Bai dace Najeriya ta fi Saudiyya arahar man fetur ba —Buhari
Jordan ta dauki matakin yi wa tattalin arzikinta garambawul ne da nufin farfado da shi daga matsi mafi tsanani da ya shiga sakamakon annobar coronavirus.
A ranar Laraba ne aka nada Khasawneh, mai shekara 51 domin ya maye gurbin Omar al Razzaz, a daidai lokacin da jama’ar kasar ke nuna bacin ransu game da kara tabarbarewar tattalin arziki.
Masu korafe-korafe a Jordan na kuma zargin gwamnati da tauye hakkin walwalar jama’a a karkashin sabbin dokokin da ta sanya da nufin dakile yaduwar cutar.