Sarauniya Elizabeth II ta cika shekara 70 a kan karagar sarautar Ingila, wadda ta hau tun tana matashiya.
Sarauniya Elizabeth II ita ce ta farko a cikin jerin sarakunan Ingila da ta shafe shekara 70 a kan karagar mulki, wanda ta hau tun tana matashiya.
- Sarauniyar Ingila da mijinta sun yi bikin cika shekara 70 da aure
- Mijin Sarauniyar Ingila, Yarima Philip ya rasu
- An sayar da wasiqar soyayya ta Sarauniyar Ingila kan Naira miliyan 64
“Sarauniya Elizabeth II, “Ita ce ta hau kan karagar mulfi dana da mafi karancin shekaru, duk da aka ta yi muki da kwarin gwiwa kuma ta sau manyan nasarori masu tarin yawa a a tsawon lokacin,” inji sakon taya murnar cikarta shekara 70 a kan karagar mulki da Shugaba Muhammadu Buhari ya aike mata.
Ya yaba mata bisa kishin da take nunawa da kuma yin aiki tukuru domin jama’arta da ma kasashen rainon Ingila.
“Mutane ba su taba karaya da Sarauniya Elizabeth II ba. Sun yi amma cewa za ta iya share musu hawaye musamman a lokacin da suke cikin damuwa.
”Wannan ya tabbatar da cewa ita a koyaushe kokari take yi domin ta sauke nauyi tare da biyan bukatun jama’a.
“A yayin da take ci gaba da wannan jagoranci, bayan rasuwar abokin rayuwarta, Yarima Philip, Duke na Edinburgh, ni da daukacin jama’ar Najeriya muna rokon Allah Ya kara mata lafiya, Ya ja kwananta a sarautar Ingila da kuma Kungiyar Kasashen Rainon Ingila”.