Sarakunan Jihar Anambra sun ziyarci Fadar Shugaban Kasa kwana guda bayan Gwamna Willie Obiano ya dakatar da sarakuna 12 saboda yin hakan.
A ganawarsu da Shugaban Ma’aikatan Shugaba Kasa, Ibrahim Gambari, a ranar Alhamis, sarakunan sun ce sun je ne domin yaba kyawawan ayyukan Shugaba Buhari a yankin Kudu maso Gabas da ma kasa baki daya.
“Yanzu ga shi Gadar Neja ta biyu da ta gagari gwamnatin baya ta kusa kammaluwa a lokacin mulikinka”, baya ga ayyukan titin Enugu-Onitsha da Inugu-Fatakwal da sauransu na daga cikin manya ayyukan da suka yaba.
“Jama’ar Kudu maso Gabas suna godiya domin ba mu taba samun haka ba, saboda haka muke cewa DAALU (mun gode) a madadinsu”, inji su.
Sarankunan sun hada da Eze Dakta Nkeli Nzekwe da Igwe Chuba Mbakwe da Igwe Chijioke Nwankwo sai Igwe Anthony Onwekwelu da kuma Igwe Chukwuma Bobo Orji.
Idan za a iya tunawa, a ranar Talata Gwamna Willie Obiano ya dakatar da sarakuna 12 wadanda Prince Arhur Eze ya jagoranta zuwa Shugaban Kasar duk da cewa ba su samu ganin Shugaba Buhari ba a ranar.
Sanarwar da Gwamnatin Jihar Anambra ta fitar ta soke duk mukaman da sarakunan ke rike da shi a gwamnati ya kuma haramta musu gabatar da kansu a matsayin masu wakiltar masarautun jihar.
Ta ce ta dauki matakin ne domin zama izna ga wasu domin fita daga jihar ba tare da sanar da gwamna ko shugaban karamar hukuma ba ya saba tsarin aikin sarakunan.