✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saraki ya fadi a zaben sanata

Shugaban  Majalisar Dattawa Bukola  Saraki ya sha kayi a zaben sanatan Kwara ta Tsakiya a hannun dan Jam’iyyar APC Dokta Yahaya Oloriegbe. Saraki ya fadi…

Shugaban  Majalisar Dattawa Bukola  Saraki ya sha kayi a zaben sanatan Kwara ta Tsakiya a hannun dan Jam’iyyar APC Dokta Yahaya Oloriegbe.

Saraki ya fadi a kananan hukomomin Asa da Ilorin ta Kudu da Ilorin ta  Gabas da Ilorin ta Yamma.

Oloriebe ya samu kuri’a 15,932, inda Saraki ya samu 11,252 a Karamar Hukumar Asa, sannan a Ilorin ta  Gabas APC ta samu 30,014 PDP ta samu 14,654, sannan kuma a Ilorin ta Kudu APC ta samu 26,331 PDP ta samu 13,013.