Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Dokta Bukola Saraki, ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari a kan cewa bai kamata a bar wa jam’iyyar APC mai mulki a kasar ragamar magance matsaloli da kasar ke fuskanta ba.
Dokta Bukola Saraki ya ce akwai bukatar gwamnatin Shugaba Buhari ta jam’iyyar APC ta hada hannu da sauran jam’iyyun hamayya domin tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta musamman matsalar tsaro.
- Gwamnati ta amince a bude cibiyoyi 774 na sabunta layin waya
- Gwamnatin Gombe ta nada sabon Mai Tangale
- An kama dalibai ’yan kungiyar asiri a Jami’ar Dutsin-Ma
Shawarar tsohon shugaban Majalisar Dattawan wanda ke zaman Shugaban Kwamitin Sulhu na jam’iyyar PDP na zuwa ne yayin da jagoranci tawagar jiga-jigan jam’iyyar da suka kai wa tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a ranar Talata.
Yayin ganawarsa da manema labarai jim kadan bayan tattaunawar sirri ta tsawon sa’a biyu a dakin karatun tsohon shugaban kasa da ke birnin Abeokuta na Jihar Ogun, tsohon gwamnan na jihar Kwara ya ce akwai bukatar gwamnatin jam’iyyar APC ta hada hannu da dukkan masu ruwa da tsaki wajen magance matsalolin da suka addabi kasar nan musamman a yankunan da ke fama da matsalar tsaro.
Saraki ya ce, “yaki da masu tayar da kayar baya ya sha gaban Buhari da jam’iyyar APC, saboda haka ya kamata Shugaban Kasa ya hada hannu da sauran jam’iyyun adawa da kasashen duniya da sauran masu ruwa da tsaki wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.”
“Wannan ita ce shawarar da ya kamata Shugaban Kasa ya dauka domin magance matsalar tsaro da sauran kalubalen da suka addabi al’umma.”
Aminiya ta samu cewa daga cikin jiga-jigan jam’iyyar PDP da suka ziyarci tsohon Shugaban kasar sun hada da tsoffin gwamnonin; Ibrahim Dankwambo (Gombe), Olagunsoye Oyinlola (Osun), Liyel Imoke (Kuros Riba), Ibrahim Shehu Shema (Katsina) da kuma tsohuwar Shugabar Masu Rinjaye a Majalisar Wakilai, Mulikat Akande Adeola.