✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanwo-Olu ya lashe kananan hukumomi 18 cikin 20

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu na Jam’iyyar APC ya ba abokan takararsa na PDP da Labour rata mai yawa a zaben Gwamnan Jihar Legas da…

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu na Jam’iyyar APC ya ba abokan takararsa na PDP da Labour rata mai yawa a zaben Gwamnan Jihar Legas da aka yi jiya Asabar.
Sanwo-Olu ya lashe kananan hukumomi 18 cikin 19 da aka sanar, inda Gbadebo Rhodes-Vivour na LP na lashe Karamar Hukuma daya ta Amuwu
-Odofin.
Yanzu saura Karamar Hukuma daya kawai ta Eti-Osa da ake jiya, wanda yanzu haka ake cigaba da tattarawa.

Zaben gwamna: APC na gaba da tazarar kuri’a 21,200 a Jihar Sakkwato
Kananan hukumomi da APC ta lashe su ne: Agege da Apapa da Lagos Island da Lagos Mainland da Alimosho da Ikorudu da Somolu da Kosofe da Ajeromi da Ifelodun da Epe da Ibeju-Lekki da Mushin da Surulere da Ikeja da Ojo da Badagry da Oshodi-Isolo.
Sakamakon ya nuna cewa LP ta rasa kananan hukumomin da ta lashe a Zaben Shugabab Kasa.
An dage sanar da sakamakon zaben zuwa karfe na yamma domin cigaba.

%d bloggers like this: