Fitaccen lauyan nan mai kare haƙƙin bil Adama, Femi Falana SAN, ya ce ya la’akari da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke a bayan nan, ya zama wajibi Sarki ɗaya tilo ne zai kasance a Jihar Kano.
Falana wanda ya faɗi hakan a cikin wani hoton bidiyo da ya karaɗe dandalan sada zumunta, ya kuma bayyana Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II a matsayin halastaccen sarki kuma zama daram duk da tababar da ake yi dangane da rikicin Masarautar Kano.
- China za ta sayar wa Elon Musk TikTok saboda rashin tabbas
- Sojoji sun haramta amfani da jirage marasa matuki a Arewa maso Yamma
Falana ya bayyana cewa “dole ne mu faɗa wa kanmu gaskiya a matsayinmu na lauyoyi. Saboda haka ina taya Mai Martaba murna dangane da nasarar da ya samu a Kotun Ɗaukaka Ƙara.
“Duk da cewa masu adawa da kai [Sarki Sanusi] sun ce za su garzaya Kotun Ƙoli, dole ne kuma mu a matsayinmu na Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) mu yi ruwa da tsaki a lamarin.
“Dole ne a fahimci tanadin da doka ta yi dangane da hurumin kowacce kotu dangane da mas’alar da ta shafi masarauta.
“Abu na biyu kuma shi ne Kotun Tarayya ba ta hurumi kan abin da ya shafi masarauta, saboda haka idan ma har akwai wasu lauyoyi da ke ganin Kotun Ƙoli na abin faɗa a wannan lamari to kuwa suna yaudarar waɗanda suke wakilta.
“Ire-iren waɗannan lauyoyi suna kawo matsala a ƙasar nan kuma nauyi ya rataya a wuyan Ƙungiyar Lauyoyin Najeriya NBA ta shiga ta yi ruwa da tsaki domin a yi wa tufkar hanci.
“Mai Martaba [Sarki Sanusi] ya sani cewa duk ma inda waɗannan lauyoyi za su je, kana nan zama daram a kujerar mulki kuma dole Sarki ɗaya tilo ne a Kano.
“Ba zai yiwu a ce akwai sarakuna biyu ba ne a Kano ko Shugaban Majalisar Dokoki biyu a Ribas. Dole ne a kawo ƙarshen wannan ruɗani.”
Ana iya tuna cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin sauraron ƙarar da ta shafi soke masarautun Jihar Kano.
Kotun a hukuncinta na farko ta ce Babbar Kotun Kano ce kawai take da damar yanke hukunci kan duk wani ruɗani da ya shafi sarauta a jihar.
Sai dai an samu saɓani tsakanin alƙalai uku da suka yanke hukunci kan lamarin.
Mai shari’a Gabriel Kolawale, wanda shi ne ya karanto hukuncin ya umarci da a mayar da ƙarar zuwa kotun da ta dace, wato Babbar kotun Kano domin ci gaba da sauraro.
Sai dai sauran alƙalan biyu sun ƙi amincewa da batun mayar da ƙarar zuwa Babbar kotun jihar Kano, inda suka bayar da umarnin watsi da batun shari’ar baki ɗayanta.
A hukunci na biyu kuma kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da matakin Babbar kotun Kano na haramta wa Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu na jihar bayyana kansu a matsayin sarakuna.
Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Mohammed Mustapha ta bayyana cewa akwai kuskure a hukuncin Babbar kotun Kano na ranar 15 ga watan Yulin 2024, kuma ya saɓa wa ƙa’idar jin ta-bakin kowane ɓangare.
Kotun ta kuma umarci alƙalin kotun ta Kano ya miƙa shari’ar ga wani alƙalin na daban domin a sake sauraron shi daga farko.
Kotun ɗaukaka ƙarar ta ce hukuncin kotun ta Kano na cike da “rashin adalci da saɓa ƙa’idar bai wa kowane ɓangare dama.”
Kotun ta ce Babbar kotun Kano ta ci gaba da sauraron ƙarar ne ba tare sanar da Aminu Ado Bayero game da ƙarar ba, kuma ba a ba shi damar gabatar da nasa hujjojin ba.
Rikicin Masarautar Kano
Rikicin masarautar Kano na baya-bayan nan ya samo asali ne daga matakin da gwamnatin jihar ta ɗauka a 2023, inda gyaran da majalisar dokokin jihar ta yi wa dokar masarautun jihar ta bai wa gwamnan jihar damar rushe masarautu biyar na jihar.
Wannan ne ya bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf damar sauke Aminu Ado Bayero da sarakunan masarautun Bichi, Gaya, Karaye da Rano daga kan muƙamansu.