✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sansanin sojin Faransa: Kotu ta tura Mahadi Shehu kurkuku

Kotu ta tura Mahadi Shehu zuwa gidan yari saboda zargin Tinubu da ba wa Faransa izinin kafa sansanin soji a Arewacin Najeriya

Kotu ta ba da umarnin tsare wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Mahadi Shehu, a gidan yari.

A ƙarshen mako ne Hukumar Tsaron ta DSS ce ta tsare Mahadi Shehu a Kaduna, bayan ya wallafa wani bidiyo tare da iƙirarin cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sahale wa Faransa kafa sansanin soja a Arewacin Najeriya.

A cikin bidiyon, wanda daga baya aka goge, an ga wani hafsan sojan Najeriya yana magana da harshen Hausa, da wani sojan ƙasar waje a bayansa.

Tuni dai Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro Nuhu Ribadu da Ministan Yaɗa Labarai Mohammed Idris suka ƙaryata iƙirarin na Mahadi a matsayin mara tushe.

Binciken da aka gudanar kan bidiyon da Mahadi Shehu ke iƙirarin sojojin Faransa sun je Jihar Borno domin kafa sansanin soji, ba gaskiya ba ne.

A ranar Talata DSS ta gurfanar da Mahadi Shehu a gaban Mai Shari’a Abubakar Lamiɗo na Babbar Kotun Jihar Kaduna, kan zargin taimaka wa ta’ddanci da tayar da hankalin jama’a.

“Mai Sharia Lamiɗo ya ba da umarnin a ci gaba da tsare Mahadi a gidan yari har zuwa ranar 14 ga watan Janairu, 2025 da muke ciki,” in ji sanarwar da hukumar DSS ta fitar.