✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sannu a hankali Najeriya na komawa mulkin kama-karya – Jonathan

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce sannu a hankali Najeriya ta fara komawa mulkin kama-karya. Ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekara…

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya ce sannu a hankali Najeriya ta fara komawa mulkin kama-karya.

Ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekara 70 na Bishop din darikar Katolika na Sakkwato, Matthew Hassan Kukah, wanda aka gudanar a otal din Sheraton da ke Abuja ranar Laraba.

Da yake jawabi a taken taron, ‘Girman Najeriya bai kare ba: Mataki na gaba,’ Jonathan ya bukaci ’yan Najeriya da su yi taka-tsan-tsan tare da hada kai wajen zabar shugabannin da za su jagoranci al’ummar kasar nan zuwa samar da kasar da za ta yi alfahari da kanta. 

Ya ce, “Aikin da ke gabanmu ba shi ne mu yi rauni da masu tsaronmu ba, don kada dimokuradiyyar da muke takama da ita a yau, ta fada cikin barazana ta koma baya a gobe, kuma akwai alamun hakan.

“Idan muka dubi jahohi da sauransu, muna karkata zuwa ga tsarin mulkin kama-karya, amma dimokuradiyya ba wai cin zabe kadai ba ne, batun dauwama ne kan turba.

“Mu a matsayinmu na shugabanni a matakin kasa da kuma a matakin jihohi, musamman a wannan lokaci da zabe ke tafe, dole ne mu dauki ra’ayoyi daban-daban.”

Jonathan ya kuma bukaci matasan da suka yi rajistar zaben 2023 da su yunkura su yi aiki da aniyarsu ta hanyar tabbatar da cewa sun kada kuri’a a ranar zabe.

Sauran manyan baki a wajen taron sun hada da dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu da Mataimakin takararsa, Sanata Kashim Shettima da Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi da na jihar Filato, Simon Lalong da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha.

Sauran sune Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da na jihar Ogun, Dapo Abiodun da na Akwa Ibom, Udom Emmanuel da tsohon Gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha da tsohon Gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson.