Kungiyar Sanatocin Arewa ta buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta maido da wutar lantarki a jihohin Kano, Kaduna, Katsina, Jigawa da sauran jihohin Arewa.
Sanatocin sun buƙaci Gwamnatin Tarayyar ta gaggauta gyara layukan samar da wutar na Shiroro zuwa Kaduna domin dawo da wutar lantarkin a Arewacin ƙasar.
- Zaɓen Ƙananan Hukumomi: An kammala kaɗa ƙuri’a a wasu yankunan Kano
- ‘Hukunta duk wanda ya yi wa PDP zagon ƙasa ya zama dole’
Sanarwar da Shugaban Ƙungiyar Sanatocin Arewa, Sanata Abdulaziz Yar’adua ya sanya wa hannu bayan ganawar da suka yi ranar Asabar a Abuja, ta kuma bukaci gwamnati ta aiwatar da matakan daƙile ɓarnar da kayayyakin lantarkin a Arewacin ƙasar nan gaba.
Aminiya ta ruwaito cewa, wasu sassan Arewa na cikin duhu, biyo bayan wata matsalar da aka samu a layin wutar lantarki mai karfin 330kV.
Lamarin dai ya haifar da katsewar wutar lantarki a yankin Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma da kuma wasu sassan Arewa ta Tsakiya, ya shafi layin da ya kamata ya zama madogarar samar da wutar lantarki ga jihohin da ke ƙarƙashin kamfanin wutar lantarki na Kaduna da Jos da Kano.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Harkokin kasuwanci sun tsaya a sakamakon matsalar lantarkin da ake fuskanta wanda ya jefa tattalin arziki cikin garari haɗi da tabarbarewar harkokin kiwon lafiya alhali ana fama da tsadar mai a ƙasar.
“Masu ƙananan kasuwanci na kokawa da yadda harkoki suka kasamce, asibitoci na fuskantar tsadar tafiyar da harkokin al’amuransu sannan kuma muhimman abubuwan buƙata na rayuwa an yi musu illa.
“Kungiyar Sanatocin Arewa cikin mutuntawa tana roƙon Gwamnatin Tarayya da ta kara ƙaimi tare da ba da fifiko wajen gyaran layukan wuta na Shiroro zuwa Kaduna domin dawo da ingantaccen wutar lantarki.
“Kungiyar ta amince da ci gaban da aka samu wajen rabon wutar lantarki a karkashin gwamnati mai ci kuma ta yaba da kokarin da ake na inganta fannin.
“Sai dai lamarin na bukatar kulawar gaggawa domin rage wahalhalun da jama’a ke fuskanta da kuma farfado da harkokin tattalin arziki.”