✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sanatoci 3 da har yanzu ba a maye gurbinsu ba bayan watanni 9 da murabus

Ba mu da wata matsala da matakin INEC kan jinkirin gudanar da zaben cike gurbi.

Har yanzu babu wadanda suka maye gurbin Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, da mataimakinsa na shiyyar Arewa, Sanata Abubakar Kyari, da Mataimakin Gwamnan Zamfara, Sanata Muhammad Nasiha a Majalisar dattawa bayan shafe watanni tara da yin murabus daga kujerunsu.

Gabanin karbar mukamansu na yanzu, Sanata Adamu shi ke wakiltar Nasarawa ta Yamma a majalisa, sai Kyari da ke wakiltar Borno ta Arewa, hadi da Nasiha da ke wakiltar Zamfara ta Tsakiya.

Aminiya ta binciko yadda rashin cike wannan gurbi ya sanya al’ummar da ke mazabun rasa wakilci a majalisar.

Wannan dai ba shi da wata nasaba face ta rashin shirya zaben cike-gurbi da Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta yi kan kujerun.

Sai dai gabanin Babban Zaben kujerun Shugaban Kasa da ’yan majalisu da za a gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, an samu wadanda suka fito takarar kujerun a jam’iyyu daban-daban.

Sashi na 68 na kyundin Tsarin Mulki na 1999 ya bayyana hanyoyin da za a bi wajen cike guraban kujerun majalisar.

Sashi na 68 (1) ya ce dan Majalisar Dattawa ko na Majalisar Wakilai zai iya barin matsayin idan ya zamo mamba na kwamiti ko wata hukuma da Kundin Tsarin Mulkin ko wata doka ymta kafa.

Sai dai mai magana da yawun jam’iyyar APC a Jihar Zamfara, Yusuf Idris Gusau ya ce ba su da wata matsala da matakin INEC din na jinkirin gudanar da zaben.

Yunkurin da muka yi na ji bakin Shugaban Kwamitin Yada Labarai da Wayar da Kan Masu Kada Kuri’a na INEC, Barista Festus Okoye, ya ci tura, bayan shaida wa Aminiya cewa ba zai iya cewa komai ba a kan lamarin, har sai bayan gudanar da taron jagororin hukumar.

Sai dai wasu jami’an hukumar uku da suka nemi a sakaya sunasu sun ce Shugaban Majalisar Dattawan bai bayyana kujerun a matsayin wadanda ba su da masu rike su ba a hukumance.

Daga Abdullateef Salau (Abuja) da Hamisu K. Matazu (Maiduguri) da Shehu Umar (Gusau) da Rahima Shehu Dokaji