✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanatan Zamfara ta tsakiya ya koma APC

APC ta gudanar da taron bikin karbar Gwamnan Jihar da Sanatan.

Sanata mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya, Hassan Mohammad Gusau, ya gabatar da takardar ficewarsa daga jam’iyyar PDP, ina ya sauya sheka zuwa APC.

Sanatan ya aike da takardar tasa ce ga Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, wanda ya karanta a yayin zaman Majalisar a ranar Talata.

  1. ‘Najeriya ce ta fi yawan yara marasa zuwa makaranta’
  2. Ba zan taba bari Iran ta mallaki makamin Nukiliya ba – Biden

A cikin takardar, dan Majalisar ya bayyana cewa, “Na yanke hukuncin barin jam’iyyar saboda koma-bayan dimokuradiyya da rarrabuwar kai da ake samu a tsakanin mambobinta tun daga matakin mazabu a Jihar Zamfara.

“Zan sanar da Majalisa makomata a siyasa da kuma jam’iyyar da zan koma nan da wani lokaci,” cewar takardar.

Sanata Nasiha bi sahun Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, wajen canja sheka zuwa APC a ranar Talata.

Sauyin sheka da ’ya’yan jam’iyyar PDP ke yi a baya-bayan nan na ci gaba da daukar hankali a siyasar Najeriya.