✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanata ya raba wa ’yan mazabarsa motoci 50 da babura 500 a Gombe

Sanata mai wakiltar mazabar Gombe ta Arewa a Majalisar Dattijai, Sa’idu Ahmed Alkali, ya raba motoci da babura da injinan ban ruwa ga al’ummar mazabar…

Sanata mai wakiltar mazabar Gombe ta Arewa a Majalisar Dattijai, Sa’idu Ahmed Alkali, ya raba motoci da babura da injinan ban ruwa ga al’ummar mazabar da yake wakilta.

Sanatan dai ya raba motoci 50 ne da babura 500 da injinan ban ruwa na noman rani guda 600 da kekunan dinki da firji 600 ga mata da ke mazabar tasa.

A cewar dan majalisar, cikin ayyukan da ya gudanar a yankin sa baya ga raba tallafin sun hada da kai rokon na musamman na hukumomin asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya da ke Gombe na samar musu da hanyoyi, kuma tuni aka kammala su.

Baburan da Sanatan ya raba a Gombe
Baburan da Sanatan ya raba a Gombe

A cewarsa yanzu haka yana shirye-shiryen samar wa da asibitin karin mashiga da za ta tafi zuwa dakin kwantar da marasa lafiya na gaggawa na asibitin.

Ya kuma bayyana wasu ayyuka da dama da ya gudanar a Kananan Hukumomi biyar da suke karkashin mazabarsa da suka hada da Dukku, Funakaye, Gombe, Kwami da kuma Nafada, inda ya samar musu da cibiyoyin kula da lafiya da azuzuwan karatu da rijiyoyin burtsatse na zamani da masu aiki da hasken rana da na’urorin rarraba wutar lantarki a wasu yankunan karkara.

Da yake nasa jawabin, Shugaban majalisar Dattawan, Sanata Ahmed Lawan, wanda ya halarci bikin raba kyayyakin, kiran al’ummar mazabar ya yi da su ci gaba da mara wa Sanata baya saboda mutum ne mai hazaka da son jama’arsa .

Shi ma Gwamnan Jihar, Inuwa Yahaya, ya jinjina wa Sanatan bisa wannan hobbasa na tallafawa al’ummarsa, yana mai yin kira ga sauran ’yan majalisa da su yi koyi da shi.

%d bloggers like this: