✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Sanata Elisha Abbo ya fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC

Sanata Elisha Abbo, mai wakiltar shiyyar Adamawa ta arewa a Majalisar Dattawa, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC. Sanata Elisha ya bayyana hakan…

Sanata Elisha Abbo, mai wakiltar shiyyar Adamawa ta arewa a Majalisar Dattawa, ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sanata Elisha ya bayyana hakan ne cikin wata wasika da ya aike wa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, wacce aka karanta yayin zaman majalisar na ranar Laraba.

“Na rubuta wannan takarda ne domin sanar da Shugaban Majalisa da ’yan Najeriya cewar na sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC.

Sanata Abbo ya bayyana cewa ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP ne saboda rashin kyakkyawan shugabanci da Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ke yi a jiharsa ta Adamawa, wanda kuma a cewarsa hakan ya janyo rarrabuwar kawuna a jam’iyyar a jihar.

Ya kuma ce ya yi hakan ne saboda irin ayyukan ci gaba da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ke yi na tallafa wa rayuwar matasa.

Ya zuwa yanzu, sanatocin da jam’iyyar APC mai mulki ke da su a Majalisar Dattawa sun kai 60, yayin da ita kuma adawa ta PDP ke da 42.