✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Coronavirus ta kashe Sanata Buruji Kashamu

Mamacin shi ne dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Ogun a 2019

Sanata Buruji Kashamu ya riga mu gidan gaskiya bayan fama da cutar coronavirus.

Sanata Ben Murray Bruce ya sanar da rasuwar tasa ta shafinsa na Twitter a Yammacin Asabar 8 ga Agusta, 2020.

“Abokina na kut-da-kut Sanata Buruji Kashamu ya rasu sakamakon COVID-19 a asibitin First Cardiology Consultants da ke Legas”, inji shi.

Ya kuma mika jajensa ga iyalan mamacin, wanda shi ne dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP a jiharsa ta Ogun a zaben 2019.

Marigayi Buruji babban jigon jam’iyyar PDP ne a yankin Kudu maso Yamma kuma tsohon shugaban kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar a yankin.

Shi ne kuma tsohon Mataimakin Shugaban Kwamitin Jihohi da Kananan Hukumomi a Majalisar Dattawa ta takwas.

A 2018 jam’iyyar ta taba koran shi kafin daga baya wata Babbar Kotun da ke zamanta a Abuja ta soke hukuncin a cikin shekarar.

Yanzu Buruji Kashamu wanda aka haifa a shekarar 1958, na daga cikin fitattun mutane a Najeriya da cutar COVID-19 ta yi ajalinsu tun bayan bullarta a watan Fabrairu.